Menene Amfanin Ararrabi Ga Mutum

Gabatarwa 

Shi Ararrabi wata bishiyace da akafi samun ta a kasashen afrika ta yamma, kuma amfanin ararrabi ba zasu misaltu ba.

Ana iya samun ararrabi a kasar India da kuma kasashen larabawa. 

Haka zalika, ana amfani da bawon jikin wannan bishiya da kuma ganyen ta wajen dakile cuta a jiki. 

Tarihi ya nuna cewa mutane sunyi amfani dashi a shekaru masu dunbin yawa da suka wuce. 

Shi ganyen ararrabi yana da tasiri akan amosanin gabbai, cutar da za tasa hanji ya kumbura, cutar asma da kuma cututtuka masu dama.

Bawon mainan ararrabi yana taimakawa sosai wajen rage kumburi a jiki.

Ilimin hikima ya fara bayyana amfanin ararrabi a jiki. Amma har yanzu, ba a samu takamaiman binciken da ya nuna tabbacin amfanin ararrabi ba. 

An jarraba sassaken ararrabi da kuma ganyen wannan bishiya akan dabbobi domin a gano dumbin amfanin sa ga mutum.

Ana samun man ararrabi domin amfani dashi a fata.

Yana da muhimmanci ka fara tuntubar likitanka, kafin ka fara amfani da ararrabi.

Nigella Sativa: Everything About Habbatus Sauda (Habbatus Soda)

Yanayin Tsarin Bishiyar Ararrabi

Ita bishiyar ararrabi tana da tsayi wanda yakai mita goma sha uku (13m). Tana fitar da kyawawan furanni masu matukar kamshi. 

Ita wannan bishiya tana maganin cututtuka masu dama kamar su zazzabin cizon sauro, ciwon daji, ciwon sukari da sauransu.

17 Awesome Health Benefits of Guinea Corn and Millet

Yadda Zaka Samu Ararrabi 

Saboda amfanin ararrabi da bazasu kididdigu ba, ana samunsa a kauyuka da kuma gonaki. 

Ana samun maganin ararrabi a gidaje, gonaki da kuma kasuwanni musamman a arewacin Najeriya. 

Ita wannan bishiya tafi yawa a kauyuka saboda girman bishiyar. Zaka sameshi tsilla tsilla a cikin birane.

20 Worst Foods to Eat During Pregnancy

Amfanin Ararrabi 

 1. Mutanen arewacin najeriya suna amfani da tushen wannan bishiya wajen warkar da rauni.
 1. Ana ararrabi da zobo dan samu lafiya daga cutar syphilis. 
 1. Ana amfani da ararrabi wajen kashe kwayoyin cututtuka da kuma gida
 1. Bawon jikin bishiyar ararrabi yana da muhimmanci wajen dakile cutar olsa, zafin ciki, da kuma gudawa. 
 1. Ararrabi yana taimakawa wajen kashe kwayoyin cuta na bakteriya. 
 1. Bincike ya nuna cewa tsantsar ɗanyen itacen ararrabi yana kashe ƙwayoyin cuta ta ƙwayoyin gram-positive da gram-negative
 1. Ana amfani da ararrabi domin samun waraka wajen ciwon raunin kwakwalwa. 
 1. Zaku iya amfani da ararrabi wajen kumburin gabobi.
 1. Ararrabi yana da muhimmanci wajen ciwon zazzabin hay, ciwon daji, ciwon sukari 
 1. Yana taimakawa wajen ciwon jinin haila 
 1. Wannan magani, yana taimakawa kwarai wajen kara kuzari a wajen motsa jiki.
 1. Ana amfani da ararrabi domin kara karfin tunkudowar fitsari.
 1. Ana amfani da a ararrabi domin rage kurajen fuska. 
 1. Yana da tasiri akan hana tsufan wuri ga wadanda suke shafawa a fuska.
 1. Yin amfani da ararrabi yana da tasiri wajen dakile cutar daji. Baya da haka, yana hana enzymes wajen lalata DNA.
 1. Ararrabi yana taimakawa wajen warkar da cutar da take raunana sassan jiki da kuma jijiyoyin da suke sarrafasu (parkinson’s disease)
 2. Ita wannan bishiya tana maganin zazzabin taifot
 3. Tana da matukar tasiri akan cutar hanta
 4. Yana hana dafin maciji yayi tasiri a jikin mutum

Important Health Benefits of Mixing Rice and Beans

Yadda za ayi Amfani da Ararrabi 

Yana da matukar muhimmanci ka samu likita kafin ka fara amfani da ararrabi. Wannan

Cibiyar Arthritis sun ba da shawarar amfani da nauyin mili gram dari uku ko dari hudu a rana. 

Ana samun maganin ararrabi a matsayin kwayar magani a shagunan sai da magani. Ku tabbatar kunyi amfanin da shawarar likita kafin kuyi amfani dashi. 

Ararrabi yana iya haifar da matsala idan aka hadashi da wadannan magungunan:

 • Aspirin 
 • Naproxen
 • Ibuprofen 

 

Zaku iya hada ararrabi da namijin goro bayan an dakasu, sai a bawa wanda maciji ya sara.

13 Important Foods That Will Provide You With Adequate Vitamin C

Mummunan Tasirin Ararrabi

Shan ararrabi ba tare dabin ka’idaba yana iya haifar da:

 • Zubar da ciki saboda fitar jini 
 • Tashin Zuciya 
 • Gudawa
 • Lalacewar fatar jiki GA wasu mutanen. 

References

 1. First Reference

2. Second Reference

3. Third Reference

About the author

Arewagist

View all posts

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *