amafanin kuka da madara
amafanin kuka da madara

Menene Amfanin kuka da Madara a Jikin Mutum.

Gabatarwa

 

Amfanin kuka da madara a jikin ɗan Adam bazasu ƙirguba. Saboda kuka tana da matuƙar muhimmanci wajen kariya daga cutar zazzabin cizon sauro, tarun fuka, ƙwayoyin cutar da ake iya dauka, gudawa, cutar anemiya, ciwon ciki da kuma hakori. 

 

Haka zalika madara, ta ƙunshi abubuwan gina jiki masu ɗumbin muhimmanci. Ire-iren abubuwan da zaka samu daga kofi daya (244 grams) na madara, ya haɗa da:

 

 • Abinci mai gina jiki (protein) -8 grams 
 • Abinci mai bada ƙarfin jiki (calories) – 146
 • Man kitse (Fat) – 8 grams 
 • Kalsiyum (calcium) – 28%
 • Vitamin B2 – 26%
 • Vitamin B12 – 18%
 • Vitamin D – 24%
 • Potassium – 10%
 • Phosphorus – 22%
 • Selenium – 13% 

 

Madara ta tanadi bitamin A, magnesium, zinc da kuma thiamine (B1).

 

Boswellia dalzielii: Amfanin Ararrabi Masu Muhimmanci a Jiki

Menene kuka? 

 

Kuka wata bishiyace mai matsanancin girma da tarihi. Ana samun ita wannan bishiya a kasashen Afrika, Ostreliya (Australia), Madagaska (Madagascar) da kuma kasashen yankin Asiya (Asia).

 

Wasu suna kiranta da suna Adansonia. Wannan suna ya samo asaline daga wani bafaranse (Dan kasar farans) saboda aikin bincike da yayi akan ita wannan bishiya. 

 

Ita wannan bishiya tana da kyawawan furanni waɗanda suke ɗaukar tsawon sa’o’i 15.

 

Su waɗannan furen, suna fitowa a lokacin yammaci, sa’annan su zubo a ƙasan bishiyar kuka da safe. 

 

Hanyoyin Kariya Daga Matsalar Gas din Dafa Abinci

Asalin Kuka da Kuma Yadda Ake Shukata

 

Hanyar shuka ita wannan bishiya mai dumbin muhimmanci shine, ta hanyar shuka ƙwayar tsaba na kuka. 

 

Da farko zaka saka ƙwayar tsaban a cikin ruwa ya kwana. Sa’annan, sai ka samu ka fitar da farin kwayar da yake ciki. 

 

Zaka bar kwayar ta bushe har kimanin kwana daya. 

 

Ya kamata ka shuka kamar kwaya uku, domin ba lallai gaba ɗayansu su fitoba. 

 

Yana da muhimmanci ka shuka ƙwayar sama da Inci daya ko biyu. Kada ka bari zafin kasar ya wuce digiri goma sha biyar (15). 

 

Ka tabbatar kasar da zaka shuka tana da damshi amma kada abarta ta jiƙe da ruwa.

 

A lokacin da kuka ta fara tsurowa, za a iya fitar da ita zuwa kan kasa ko kuma a saka ta a tukunya.

 

Ita kuka ana iya shukata a cikin tukunya kafin ta fara girma. A lokacin da takai yadda ya kamata a mayar da ita kan kasa, sai a cireta daga cikin tukunya a cikin nutsuwa, a tona rami a binne tushen ta a cikin kasa.

 

Ita wannan bishiya ta kuka tana rayuwa akan kowacce irin kasa, tana kuma da juriyar zafi. Bishiyar kuka tana iya ajiye ruwa akan lokaci mai tsayi, shiyasa take iya rayuwa a lokacin fari.

 

Aure: How to Plan a Hausa Wedding in the Arewa

A Ina Zaka iya Samun Kuka 

 

Ana iya samun bishiyar kuka a yankin Afrika, Asiya, Madagaska, da kuma Ostreliya.

 

Haka zalika, ana samun ta a arewacin Najeriya da kuma Nijar.

Yayan kuka

 

Yayan kuka sun tanadi bitamin C, potassium, carbohydrates, da phosphorus, carbohydrates, fiber, abincin gina jiki (protein), Man kitse (lipids)

 

Ganyen Kuka 

 

Ganyen kuka yana da amfani matuka. Yana da amfani ya hanyar:

 

 • Samun sauki wajen narkewar abinci 
 •  Taimako ta wajen rigakafi da kuma samun karfin dakile cututtuka. 
 •  Samar da isashshen ruwa a jiki 
 • Kyautata lafiyar fata 
 • Tana taimakawa wajen rigakafi a cutar asma. 

 

A arewacin Najeriya ana daka ganyen kuka domin ayi miya dashi. 

 

Amfanin Madara a Jikin Mutum 

 

Shi amfanin madara ya kunshi:

 1. Shan madara yana sanya lafiyar kashi. Saboda ta kunshi calcium, potassium, vitamin k2, phosphorus, da kuma abincin gina jiki (protein).
 2. Madara tana taimakawa wajen rage kiba. Da akwai abinda ake Kira linoleic acid a cikin madara, yana taimakawa wajen farfasa man kitse a jikin mutum. 
 3. Amfanin madara ya kunshi lafiyar hakori saboda calcium din da yake ciki. 
 4. Ita madara tana taimakawa wajen sa rauni ya warke da wuri. 
 5. Madara tana taimakawa wajen karin lafiyar bugun zuciya
 6. Shan madara zai sa jikin mutum ya samu rigakafi da cututtuka. 

 

Yadda Zaku Hada Kuka da Madara 

 

 • Ana iya zuba garin kuka a cikin abinci kamar su smuzi, da kuma salad.
 • Ana iya zuba kuka da Madara a cikin Koko 
 • Ana iya hada kuka da Madara a cikin ruwa, sa’annan a sa zuma kadan domin sha. 

 

Amfanin Hadin kuka da Madara 

 

Akwai fa’idodi da yawa ga shan kuka da madara. Hakan yana taimakawa ta hanyar samar da ƙoshin lafiya.  

 

Madara tana sa gina jiki da kuma karfin kashi. Idan aka haɗa madara da kuka, ana iya samun abinci mai gina jiki da abubuwa masu muhimmanci a jiki. 

A Takaice 

 

 1. Bishiyan kuka wani nau’in itace ne mai ban sha’awa kuma na musamman.

 

 1. Kuka tana da fa’idodi da yawa, gami da yawan ‘ya’yan itace, tsawon rai, da juriya ga kwari da cututtuka.

 

 1. ‘Ya’yan itacen kuka abu sun shahara a Afirka da sauran sassan duniya.

 

 1. Ana amfani da itacen bishiyar kuka don sarrafa kayan daki, kayan aiki, da gine-gine.

 

 1. Itacen kuka yana samar da abinci, ruwa, da sauran albarkatu ga mutane da dabbobi.

 

Reference

 1. First 
 2. Second 

About the author

Arewagist

View all posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *