gas din dafa abinci
gas din dafa abinci

Hanyoyin Kariya Daga Matsalar Gas din Dafa Abinci

Gabatarwa

Shi gas din dafa abinci yana da matukar muhimmanci a wannan zamanin. Gas din dafa abinci yana da matukar sauki ta hanyar dafa abinci. Saboda mutane da yawa suna amfani da gas a wajen girki, yana da muhimmanci kasan hanyoyin kariya daga matsalar gas din dafa abinci.

Hakan yasa mutane da dama suna amfani dashi a maimakon gawayi, Itace, da kananzir.

Shi gas din dafa abinci ana kiransa da Liquefied Petroleum Gas (LPG) da turanci. Kuma, bature mai suna Zachäus Winzler shine wanda ya fara kera gas din dafa abinci ya kuma yi amfani dashi a shekara ta 1802.

Yana da saurin dafa abinci, sa’nnan yana sa girki yayi sauki matuka. 

Yana da muhimmanci asan hanyoyin da za ayi amfani dashi dan daga fashewa. 

Bincike ya nuna cewa mutane sama da miliyan hudune suke rasuwa saboda amfani da gas din dafa abinci. 

Dan haka, yana da muhimmanci ka kula da lafiyarka a lokacin daka fara amfani da gas din dafa abinci. 

Rashin ilimi akan yadda za ayi amfani dashi gas din girki yana daya daga cikin abubuwan dake kawo matsaloli na fashewarsa. 

Wacce Hanya Zaka bi Ka Kiyaye Fashewar Gas? 

Hanyoyin kariya daga matsalar gas din dafa abinci sun kunshi:

 1. Yana da muhimmanci a tabbatar da cewa gas din dafa abinci baya fita ta wata gurbatacciyar hanya. Ku tabbatar kun daure (sosai) duk wata hanya da kuke tunanin zai fitar da iskar gas. Idan bazaku iya ba, ku kaiwa wanda yake sayar da gas din girki dan ya daure muku.
 2. Ku tabbatar cewa baku jijjiga gas din girki sosai ba, hakan akan sa ya iya fashewa. 
 3. Ku guji ajiye gas a wajen da yake da zafi sosai, soket din wuta, da kuma karkashin rana. A tabbatar an ajiye silindan gas a wajen da yake da isashshiyar iska.
 4. A tabbatar an ajiye gas din dafa abinci a wajen da ba zai fado kasa ba. Faduwarsa na ya iya janyo fashewarsa. 
 5. A duk lokacin da kukaji warin gas, yana da muhimmanci a guji kunna wutar nefa, da kuma kyatta ashana ko kunna laita. Ku bude window, da kofa domin iskar gas din ta fice. A fita da silindar gas din waje sa’annan a duba daga inda matsalar take. Ayi amfani da kumfa ya hanyar zubashi akan silindar, za aga kwan sabulu yana tashi a daidai wajen da yake zubar fa iska. 
 6. Yana da muhimmanci a tabbatar da cewa ana gaggawar sake duk abinda ya lalace a jikin gas din girki. 
 7. Ku tabbatar kun rufe gas din girki bayan an gama amfani dashi. 
 8. Kada a bari yara su kusanci silindar gas din girki, kada a barsu suyi wasa dashi. 
 9. Kada a ajiye abubuwan da suke da saurin kama wuta kusa da gas din dafa abinci. 
 10. A kiyaye kunna gas ya jima kafin a kyatta masa ashana ko kunna masa laita.

 

Ya kamata

 1. A yawaita duba lokacin da zai dena aiki (esfayari det).
 2. A duk lokacin da ake amfani da gas din dafa abinci, a tabbatar an bude taga da kofar kicin dan iska ta samu shiga. 
 3. Kada a sanya kayan da suke da saurin kamawa da wuta a yayin day ake amfani da gas din girki. 
 4. A karanta manuwal din da silinda tazo dashi kafin a fara amfani dashi.

 

 

Ku karanta:

Boswellia dalzielii: Amfanin Ararrabi Masu Muhimmanci a Jiki

Everything You Need to Know About Yan Matan Arewa

Reference

 1. First 

Second

About the author

Arewagist

View all posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *